Haɗaɗɗiyar kwamitin majalisar dattawa da ta majalisar wakilai ta tarayya kan gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya ta amince da buƙatar ƙirƙirar sabbin jihohi guda shida a faɗin ƙasar.
Wannan matsaya ta fito ne a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu da aka gudanar a jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, tare da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu.
A cewar rahoton jaridar Daily Trust, kwamitin ya tattauna ne kan buƙatu 69 da suka haɗa da ƙirƙirar jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278.
Daga cikin waɗannan buƙatun, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi shida — ɗaya daga kowace shiyya ta ƙasar — a matsayin matakin farko kafin amincewar cikakkiyar majalisa da kuma gudanar da sauran matakai na doka.
Da zarar aka amince da wannan shawarwarin gaba ɗaya, adadin jihohin Najeriya zai ƙaru daga 36 zuwa 42 jihohi.








1 Comment
Pingback: is cenforce 100 safe