Close Menu
Zamani TVZamani TV
  • Homepage
  • Labarai
  • Labaran Kasa
  • Labaran Ketare
  • Lafiya
  • Ilimi
  • Kasuwanci
  • Siyasa
  • Nishadi
  • Wasanni
What's Hot

What a Coincidence! Elected Senator in 2007, Set to Return to the Senate in 2027, God Willing – Kauran Bauchi: By Hon Hafiz Maiauduga, PhD. CPMC. Part 4

July 12, 2026

Time to Pay Back a Tested Leader: By Hon. Hafiz Maiauduga, PhD, CPMC.

June 30, 2026

Back to the Senate: Why Bauchi South Should Put Kaura First

June 28, 2026
Facebook X (Twitter) Instagram
Trending
  • What a Coincidence! Elected Senator in 2007, Set to Return to the Senate in 2027, God Willing – Kauran Bauchi: By Hon Hafiz Maiauduga, PhD. CPMC. Part 4
  • Time to Pay Back a Tested Leader: By Hon. Hafiz Maiauduga, PhD, CPMC.
  • Back to the Senate: Why Bauchi South Should Put Kaura First
  • YANZU-YANZU: Kotu ta wanke dan sanda Abba Kyari daga gaba daya tuhume-tuhumen da ake masa
  • Residents of Styre Quarters, Zango behind IDC in Bauchi Local Government Area of Bauchi State have continued to call on governments at all levels to come to their aid.
  • Ana zargin wasu ‘yan bindiga da kashe wani shugaba a ƙauyen Zalau, cikin Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi
  • Ana zargin wasu ‘yan bindiga da kashe wani shugaba a ƙauyen Zalau, cikin Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi,
  • Wunti Al-Khair Foundation ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa matasa kan fasahohin neman aiki da ƙirƙirar kasuwanci
Facebook X (Twitter) Instagram
Zamani TVZamani TV
  • Homepage
  • Labarai
  • Labaran Kasa
  • Labaran Ketare
  • Lafiya
  • Ilimi
  • Kasuwanci
  • Siyasa
  • Nishadi
  • Wasanni
Watch On YouTube Learn More About Us
Facebook X (Twitter) Instagram
Zamani TVZamani TV
Learn More About Us
Your browser does not support the video tag.
Home » Kotu Ta Sanya Ranar 30 ga Oktoba Don Gurfanar da Mutum 5 da Ake Zargi da Cin Mutuncin Sanata Shehu Buba a Intanet
Labarai

Kotu Ta Sanya Ranar 30 ga Oktoba Don Gurfanar da Mutum 5 da Ake Zargi da Cin Mutuncin Sanata Shehu Buba a Intanet

By Zamani TVOctober 22, 202512
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn WhatsApp Reddit Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 30 ga Oktoba, 2025 domin gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargi da aikata laifin cin mutuncin Sanata Shehu Buba Umar ta kafafen sada zumunta. Sanatan shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaro da Leken Asiri.

An shirya gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Rita Ofili-Ajumogobia a ranar Talata, inda ake sa ran za su bayar da amsar tuhume-tuhumen da ake musu. Sai dai, rashin halartar alkalin ya sa aka dage shari’ar zuwa ranar 30 ga Oktoba.

Lauyan gwamnati, Anthony Egwu, da lauyoyin wadanda ake tuhuma — Hamza Dantani da Affis Matanmi, sun halarci zaman kotun.

Sunayen wadanda ake tuhuma sun hada da:

  1. Ahmed Abdulrahman (41 shekara)
  2. Daure David (35 shekara)
  3. Ishaq Muhammad (25 shekara)
  4. Abdulrashid Musa (30 shekara)
  5. Nasir Abubakar (21 shekara)

An gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume 11, da Ofishin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CR/526/2025, wadda aka rubuta ranar 3 ga Oktoba kuma aka karɓa ranar 6 ga Oktoba, 2025.

Tuhume-tuhumen sun shafi laifin cin mutunci ta kafar intanet (cyberstalking) da kuma zamba ta yanar gizo (advance fee fraud) bisa dokar Cybercrime Act 2015 (da aka gyara a 2024).

A cewar tuhumar farko, ana zargin su da yin yarjejeniya don aikata laifi na cin mutuncin Sanata Shehu Buba Umar ta hanyar intanet, wanda ya sabawa Sashe na 27(1)(b) kuma ake hukunta shi a ƙarƙashin Sashe na 21(1)(b) na dokar.

A cikin wani tuhunci na daban, ana zargin Ahmed Abdulrahman da yada wani bidiyo a TikTok da YouTube ta asusun “Kibanna Channel” inda ya zargi Sanatan da cewa “mai tallafa wa ‘yan ta’adda ne,” tare da yin kira da a bincike shi. Ana zargin ya san wannan zance ba gaskiya ba ne, amma ya aikata hakan don tayar da hankalin jama’a, sabanin Sashe na 24(1)(5) na dokar Cybercrime Act.

Haka kuma, Abdulrashid Musa da Nasir Abubakar, wadanda ake tuhuma na 4 da 5, sun nemi afuwa a bidiyo daban-daban da suka fitar bayan sun yarda da laifin cin mutuncin Sanatan Bauchi ta Kudu a kafafen sada zumunta.

Rahotanni sun nuna cewa hukumomi sun kammala bincike, kuma ana sa ran shari’ar za ta fara ne da karɓar amsar tuhume-tuhume daga wadanda ake zargi a ranar da kotu ta tsara — 30 ga Oktoba, 2025.

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Telegram Email

Related Posts

Wunti Al-Khair Foundation ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa matasa kan fasahohin neman aiki da ƙirƙirar kasuwanci

October 26, 2025

Majalisa ta amince a ƙirƙiro jihohi shida a Najeriya

October 26, 2025

Tsohon Shugaban Ƙungiyar Daliban ATBU Ya Soki Yunkurin Cire Kalmar “Technology” Daga Sunan Jami’ar

October 22, 2025

12 Comments

  1. Pingback: tadalafil vidalista 60mg

  2. Pingback: vidalista ct 20 mg

  3. Pingback: prilosec omeprazole otc

  4. Pingback: orlistat brand name

  5. Pingback: zudena 100 mg

  6. Pingback: sémaglutide oral nom commercial

  7. Pingback: semaglutide nome commerciale puntura

  8. Pingback: tadalafil female

  9. Pingback: ketorolac tromethamine guide

  10. Pingback: ivermectin PK insights

  11. Pingback: vardenafil vs sildenafil differences

  12. Pingback: orlistat fat blocking mechanism

Leave A Reply Cancel Reply

Top Posts

Wunti Al-Khair Foundation ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa matasa kan fasahohin neman aiki da ƙirƙirar kasuwanci

October 26, 2025

Elder Karofi ya caccaki Sanata Shehu Buba kan kama matasa

October 22, 2025

Kotu Ta Sanya Ranar 30 ga Oktoba Don Gurfanar da Mutum 5 da Ake Zargi da Cin Mutuncin Sanata Shehu Buba a Intanet

October 22, 2025

‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda ake Zargi da Kashe Mawakin Gargajiya

October 24, 2025
Don't Miss
Breaking News

What a Coincidence! Elected Senator in 2007, Set to Return to the Senate in 2027, God Willing – Kauran Bauchi: By Hon Hafiz Maiauduga, PhD. CPMC. Part 4

By Zamani TVJuly 12, 2026

History often presents societies with unique opportunities to reconnect with their glorious past while shaping…

Time to Pay Back a Tested Leader: By Hon. Hafiz Maiauduga, PhD, CPMC.

June 30, 2026

Back to the Senate: Why Bauchi South Should Put Kaura First

June 28, 2026

YANZU-YANZU: Kotu ta wanke dan sanda Abba Kyari daga gaba daya tuhume-tuhumen da ake masa

March 5, 2026
About Us
About Us

Zamani TV is a modern media platform dedicated to delivering credible news, engaging programs, cultural values, and quality entertainment to our audience across Nigeria and beyond.

We are committed to truth, integrity, and innovation, using television and digital media to inform, educate, and inspire society.

Zabin Edita

Rundunar ’Yan Sanda ta Kaduna Ta Ce Tsohon Gwamna El-Rufai Ya Shigo Da ’Yan Daba Da Suka Tarwatsa Taron Siyasa

August 31, 2025

DA DUMI-DIMI: Kotun Bauchi Ta Baiwa EFCC Damar Ci Gaba da Binciken Hamza Koshe da Kamfaninsa

August 28, 2025

Elder Karofi ya caccaki Sanata Shehu Buba kan kama matasa

October 22, 2025
Mafi Shahara

Zamani TV ta ƙaddamar da Sabon Shafin Labarai a Yanar Gizo

August 29, 2025

YANZU-YANZU: Kotu ta wanke dan sanda Abba Kyari daga gaba daya tuhume-tuhumen da ake masa

March 5, 2026

Wunti Al-Khair Foundation ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa matasa kan fasahohin neman aiki da ƙirƙirar kasuwanci

October 26, 2025
Copyright © 2026 Zamani TV LTD, All Rights Reserved | Designed and Developed by Abdul Tech Systems Limited.
  • Homepage
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.