Kungiyar Concerned Citizens of Bauchi State ta aika da wata takardar ƙorafi zuwa ga Shugaban Jami’ar Sa’adu Zungur da ke jihar Bauchi, kan zargin wani malami a Sashen Shari’a (Faculty of Law) na jami’ar, da laifin cin zarafin mata, yin amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, da kuma aikata rashin da’a ta fuskar aiki.
A cikin takardar ƙorafin da ta ke ɗauke da kwanan wata 14 ga Oktoba, 2025, kungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar sanar da jami’ar ne bisa zargin da ya daɗe ana yi wa malamin na yin lalata da dalibai mata da ke karatu a sashen shari’a na jami’ar.
Kungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne saboda damuwa da kare mutuncin ‘ya’ya mata da dalibai gaba ɗaya, tare da tabbatar da cewa jami’ar ta ci gaba da daidaito da mutunci a idon jama’a.
A cewar rahoton, akwai hujoji da bayanai na gaskiya da ke nuna cewa malamin yana yin amfani da matsayinsa na malami domin jan hankalin dalibai mata zuwa cikin hulɗar da ta saba doka da ɗabi’a, musamman ta hanyar yaudarar su da alkawarin taimako na ilimi ko damar aiki.
Kungiyar ta nemi hukumar jami’ar da ta gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da gaskiyar lamarin, tare da ɗaukar matakin da ya dace idan aka tabbatar da laifin.
Takardar ƙorafin ta samu sa hannun Shugaban Kungiyar Concerned Citizens of Bauchi State, Comrade A.A. Nuhu, wanda ya bayyana cewa ƙungiyar za ta ci gaba da bibiyar lamarin har sai an tabbatar da adalci ga duk ɓangarorin da abin ya shafa.







