Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan wasu muhimman dokoki guda huɗu da nufin ƙarfafa tsarin mulki, inganta masarautu, da tabbatar da walwalar ma’aikata a fadin jihar.
Daya daga cikin dokokin da aka amince da su ita ce soke dokar kafa Masarautar Sayawa da maye gurbinta da Masarautar Zaar, wacce za ta kasance da hedikwata a kauyen Mhrim Namchi da ke cikin ƙaramar hukumar Tafawa Balewa — domin amsa tsohon buƙatar al’ummar yankin.
Haka kuma, Gwamna Bala ya sanya hannu kan Dokar Kafa da Dage Sarautu, wacce ta ba da dama ga ƙirƙirar sabbin masarautu guda 13 tare da fiye da dagatai 100 a fadin Jihar Bauchi.
Bugu da ƙari, ya amince da Dokar Asusun Fansho ta Ƙananan Hukumomi, inda ya sha alwashin biyan basussukan fansho da kudaden giratuti da ake bin tsoffin ma’aikatan ƙananan hukumomi.
Sannan kuma, Gwamnan ya sanya hannu kan Dokar Ƙarin Kasafin Kuɗi ta Shekarar 2025, domin tallafawa aiwatar da muhimman ayyuka da shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin sa ke aiwatarwa.
Yayin rattaba hannu a gidan gwamnati da ke Bauchi, Gwamna Bala Mohammed ya gargadi jama’a da su guji siyasantar da sabbin dokokin, tare da umartar hukumomin tsaro da su tabbatar da bin doka da oda wajen aiwatar da su.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y. Sulaiman, ya yabawa Gwamnan bisa yadda yake amsa buƙatun al’ummomi daban-daban a jihar. Ya kuma bayyana cewa yawan jama’ar da suka halarci zaman sauraron ra’ayoyin jama’a a kan dokokin ya nuna irin kishin al’umma wajen ganin gwamnati ta isa ga ƙananan yankuna.
Trending
- YANZU-YANZU: Kotu ta wanke dan sanda Abba Kyari daga gaba daya tuhume-tuhumen da ake masa
- Residents of Styre Quarters, Zango behind IDC in Bauchi Local Government Area of Bauchi State have continued to call on governments at all levels to come to their aid.
- Ana zargin wasu ‘yan bindiga da kashe wani shugaba a ƙauyen Zalau, cikin Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi
- Ana zargin wasu ‘yan bindiga da kashe wani shugaba a ƙauyen Zalau, cikin Ƙaramar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi,
- Wunti Al-Khair Foundation ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa matasa kan fasahohin neman aiki da ƙirƙirar kasuwanci
- Majalisa ta amince a ƙirƙiro jihohi shida a Najeriya
- ‘Yan Sanda Sun Cafke Wanda ake Zargi da Kashe Mawakin Gargajiya
- Kotu Ta Sanya Ranar 30 ga Oktoba Don Gurfanar da Mutum 5 da Ake Zargi da Cin Mutuncin Sanata Shehu Buba a Intanet







