Jihar Bauchi ta cika shekaru biyu da aiwatar da gagarumin sauyi a bangaren harkokin albarkatun kasa, inda aka samu labarin sabuwar tafiya mai cike da hangen nesa, sauye-sauyen manufofi da kuma jarin da bai taba kasancewa ba a baya. A tsakiya na wannan tafiya akwai Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Daular Usmaniyya), tare da wakilinsa a bangaren, Kwamishinan Habbankunan Halittu, Hon. Muhammad Maiwada Bello.
Tun daga nada shi a watan Agusta 2023, Hon. Maiwada Bello ya kawo sabon salo a tsarin kula da albarkatun kasa a matakin jiha, inda aka farfado da bangaren da aka taba dauka marar amfani, zuwa daya daga cikin ginshikan bunkasar tattalin arzikin jihar, janyo jarin waje da kuma ci gaban mutane.
A watan Afrilu 2025, Ma’aikatar ta shirya taron horas da ma’aikata na tsawon mako biyu a Hotel Zaranda, inda aka koyar da sabbin dabarun hakar ma’adinai. Haka kuma gwamnati ta sayi kayan aiki na zamani da motoci guda hudu domin bunkasa ayyukan BOGAA da BAMSEL.
Har ila yau, an dauki sabbin ma’aikata 19 a BAMSEL/ma’aikatar da kuma 43 a Bauchi Oil & Gas Academy (BOGAA), tare da aiwatar da tsari na tabbatar da gaskiya a biyan albashi.
Wani babban nasara kuma shi ne kafa BOGAA a Alkaleri, cibiyar da ta samu sahalewar NBTE tare da hadin gwiwa da kamfanoni irin su Petro-Edu. Har yanzu, sama da dalibai 530 ne suka kammala karatu, yayin da gwamnatin jihar ta ware fiye da ₦6 biliyan domin gina sabon babban harabar makarantar.
Baya ga haka, a watan Disamba 2023, aka kafa dokar Mining Consent Letter Policy, inda aka dakatar da sarakunan gargajiya daga bayar da izinin hakar ma’adinai ba tare da kulawar gwamnati ba. Wannan ya taimaka wajen dakile barna, hana ayyukan ba bisa ka’ida ba da kuma karuwar kudaden shiga.
Ma’aikatar ta kuma fara tattara bayanan duk masu hakar ma’adinai na gargajiya tare da basu damar shiga tsarin gwamnati. Wannan ya taimaka wajen samar da ayyukan yi, karuwar kudaden shiga da kuma rage matsalolin tsaro.
Daga shekarar 2023 zuwa yanzu, sama da kamfanoni 100 aka yi musu rijista da ma’aikatar, yayin da kudaden shiga suka tashi daga sifili zuwa miliyoyin naira a kowane wata.
A gefe guda kuma, an kafa hadin gwiwa tsakanin BAMSEL da kamfanin Indiya Prompt Workman Ltd, da darajar sama da dala miliyan 5, domin bude cibiyar kasuwancin ma’adinai ta kasa da kasa a Bauchi.
Babban abin da aka fi yaba shi ne jarin sama da dala biliyan 2 da aka samu a bangaren hakar ma’adinai da masana’antu. A Toro LGA, aikin $50m Rare Earth Elements Factory ya kusa kammaluwa, yayin da a Gwana, Alkaleri LGA, ake aikin gina cibiyar siminti mai darajar $1.5bn wacce za ta samar da wutar lantarki 150 MW da dubban ayyukan yi.
A watan Mayu 2025, Hon. Bello ya jagoranci tawagar jihar zuwa babban taron hakar ma’adinai na CIM CONNECT a Montreal, Kanada, tare da wasu kasashe kamar China da Afirka ta Kudu, inda aka kara fito da Bauchi a matsayin daya daga cikin wuraren da ake sa ran samun manyan jarin kasa da kasa.
Da yake magana, Hon. Bello ya ce:
“Wadannan ayyuka ba wai kawai ayyukan yau da kullum ba ne, su ne ginshikan gado da za su tabbatar da makomar Bauchi a doron cigaba, dorewa da kirkire-kirkire.”
A halin yanzu, masana harkokin ma’adinai na ganin Bauchi a matsayin jagora a fagen hakar ma’adinai a Najeriya, abin da suka danganta da hangen nesa da jagorancin Gwamna Bala Mohammed da kuma kwazon Kwamishina Maiwada Bello.







